Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 0:48

[1] Na tā da idanuna gare ka, gare ka da kursiyinka yake cikin sama.

[2] Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu, kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta, haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu, sai ya nuna mana jinƙansa.

[3] Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, gama mun jimre da reni mai yawa.

[4] Mun jimre da wulaƙanci daga masu girman kai, reni mai yawa daga masu fariya.

Zabura — Chapters