Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 0:59

[1] Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai, ta ina ne taimakona zai zo?

[2] Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, wanda ya kafa sama da ƙasa.

[3] Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;

[4] tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barci.

[5] Ubangiji yana tsaronka, Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;

[6] rana ba za tă buge ka cikin yini ba balle wata da dare.

[7] Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa, zai tsare ranka;

[8] Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka yanzu da har abada kuma.

Zabura — Chapters