[1] Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa.
[2] Na gan ka a wuri mai tsarki na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka.
[3] Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka.
[4] Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.
[5] Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.
[6] A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare.
[7] Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka.
[8] Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni.
[9] Su da suke neman raina za su hallaka; za su gangara zuwa zurfafan duniya.
[10] Za a bayar da su ga takobi su kuma zama abincin karnukan jeji.
[11] Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah; dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi, amma za a rufe bakunan maƙaryata.