Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:59

[1] Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah, dukan duniya!

[2] Ku rera ɗaukaka ga sunansa; ku sa yabonsa yă zama da ɗaukaka!

[3] Ku ce wa Allah, “Ayyukanka da banmamaki suke! Ikonka da girma yake har abokan gābanka suna durƙusa a gabanka.

[4] Dukan duniya sun rusuna a gabanka suna rera yabo gare ka, suna rera yabo ga sunanka.” Sela

[5] Ku zo ku ga abin da Allah ya yi, ayyukansa masu banmamaki a madadin mutum!

[6] Ya juya teku zuwa busasshiyar ƙasa, sun wuce cikin ruwaye da ƙafa, ku zo, mu yi farin ciki a cikinsa.

[7] Yana mulki har abada ta wurin ikonsa, idanunsa suna duban al’ummai, kada ’yan tawaye su tayar masa. Sela

[8] Ku yabi Allahnku, ya mutane, bari a ji ƙarar yabonsa;

[9] ya adana rayukanmu ya kuma kiyaye ƙafafunmu daga santsi.

[10] Gama kai, ya Allah, ka gwada mu; ka tace mu kamar azurfa.

[11] Ka kawo mu cikin kurkuku ka kuma jibga kaya masu nauyi a bayanmu.

[12] Ka bar mutane suka hau a kawunanmu; mun bi ta wuta da ruwa, amma ka kawo mu zuwa wurin yalwa.

[13] Zan zo haikalinka da hadayun ƙonawa zan kuwa cika alkawurana gare ka,

[14] alkawuran da leɓunana suka yi alkawari bakina kuma ya faɗa sa’ad da nake cikin wahala.

[15] Zan miƙa kitsen dabbobi gare ka da kuma baye-baye na raguna; zan miƙa bijimai da awaki. Sela

[16] Ku zo ku saurara, dukanku waɗanda suke tsoron Allah; bari in faɗa muku abin da ya yi mini.

[17] Na yi kuka gare shi da bakina; yabonsa yana a harshena.

[18] Da a ce na ji daɗin zunubi a zuciyata, da Ubangiji ba zai saurara ba;

[19] amma tabbatacce Allah ya saurara ya kuma ji muryata a cikin addu’a.

[20] Yabo ga Allah, wanda bai ƙi addu’ata ba ko yă janye ƙaunarsa daga gare ni!

Zabura — Chapters