Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:15

[1] Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni? Me ya sa ka yi nisa da cetona, ka yi nesa daga kalmomin nishina?

[2] Ya Allahna, na yi kuka da rana, amma ba ka amsa ba, da dare kuma ban yi shiru ba.

[3] Duk da haka kana a kursiyi a matsayin Mai Tsarkin nan; kai ne yabon Isra’ila.

[4] A gare ka ne kakanninmu suka sa bege; sun dogara ka kuwa cece su.

[5] Sun yi kuka gare ka suka kuma sami ceto; a gare ka suka dogara kuma ba su sha kunya ba.

[6] Amma ni dai tsutsa ne ba mutum ba, wanda mutane suke yi wa ba’a suka kuma rena shi.

[7] Duk wanda ya gan ni yakan yi mini ba’a; suna yin mini ashar, suna kaɗa kansu suna cewa,

[8] “Ya dogara ga Ubangiji; bari Ubangiji yă cece shi. Bari yă cece shi, da yake yana jin daɗinsa.”

[9] Duk da haka ka fitar da ni daga ciki; ka sa na dogara gare ka, ko ma a ƙirjin mahaifiyata.

[10] Daga haihuwa an jefa ni a kanka; daga cikin mahaifiyata kai ne Allahna.

[11] Kada ka yi nesa da ni, gama wahala na kusa kuma babu wani da zai taimaka.

[12] Bijimai masu yawa sun kewaye ni; bijimai masu ƙarfi na Bashan sun sa ni a tsaka.

[13] Zakoki masu ruri suna yayyage abin da suka kama sun buɗe bakunansu a kaina.

[14] An zubar da ni kamar ruwa, kuma dukan ƙasusuwana sun fiffito daga mahaɗai. Zuciyata ta zama kaki; ta narke a cikina.

[15] Ƙarfina ya bushe kamar kasko, harshena kuma ya manne wa dasashina na sama; ka kwantar da ni a ƙurar mutuwa.

[16] Karnuka sun kewaye ni; ƙungiyar mugaye sun sa ni a tsaka, sun soki hannuwana da ƙafafuna.

[17] Zan iya ƙirga ƙasusuwana; mutane suna farin ciki a kaina.

[18] Sun raba rigunana a tsakaninsu suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigunana.

[19] Amma kai, ya Ubangiji, kada ka yi nisa; Ya Ƙarfina zo da sauri don ka taimake ni.

[20] Ka ceci raina daga takobi, raina mai daraja daga ikon karnuka.

[21] Ka cece ni daga bakin zakoki; ka cece ni daga ƙahonin ɓauna.

[22] Zan furta sunanka ga ’yan’uwana; cikin taron masu sujada zan yabe ka.

[23] Ku da kuke tsoron Ubangiji, ku yabe shi! Dukanku zuriyar Yaƙub, ku girmama shi! Ku girmama shi, dukanku zuriyar Isra’ila!

[24] Gama bai rena ko yă ƙyale wahalar masu shan wuya ba; bai ɓoye fuskarsa daga gare shi ba amma ya saurari kukansa na neman taimako.

[25] Daga gare ka yabona yake zuwa cikin babban taro; a gaban waɗanda suke tsoronka zan cika alkawarina.

[26] Matalauta za su ci su ƙoshi; su da suke neman Ubangiji za su yabe shi, bari zukatanku su rayu har abada!

[27] Dukan iyakokin duniya za su tuna su kuma juya ga Ubangiji, kuma dukan iyalan al’ummai za su rusuna a gabansa,

[28] gama mulki na Ubangiji ne kuma yana mulki a bisa al’ummai.

[29] Dukan attajiran duniya za su yi biki su kuma yi sujada; dukan waɗanda suka gangara zuwa ƙura za su durƙusa a gabansa, waɗanda ba za su iya bar kansu da rai ba.

[30] Zuriya masu zuwa za su yi masa hidima; za a faɗa wa zuriya na nan gaba game da Ubangiji.

[31] Za su yi shelar adalcinsa ga mutanen da ba a riga an haifa ba, gama ya aikata shi.

Zabura — Chapters