Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:19

[1] Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.”

[2] Ubangiji zai fadada ikon sandan mulkinka daga Sihiyona za ka yi mulki a tsakiyar abokan gābanka.

[3] Rundunarka za su so yin yaƙi a ranarka ta yaƙi. Saye cikin ɗaukaka mai tsarki, daga cikin ciki na safiya za ka karɓi raɓar ƙuruciyarka.

[4] Ubangiji ya rantse ba zai kuma canja zuciyarsa ba, “Kai firist ne har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”

[5] Ubangiji yana a hannun damanka; zai murƙushe sarakuna a ranar fushinsa.

[6] Zai hukunta al’ummai, yana tarawa gawawwaki yana kuma murƙushe masu mulkin dukan duniya.

[7] Zai sha daga rafin da yake kusa da hanya; saboda haka zai ɗaga kansa sama.

Zabura — Chapters