[1] A gare ka Ya Ubangiji, na miƙa raina.
[2] A gare ka na dogara, ya Allahna. Kada ka bari in sha kunya, ko ka bar abokan gābana su yi nasara a kaina.
[3] Ba wanda yake sa bege a gare ka da zai taɓa shan kunya, amma za su sha kunya su da suke tayarwa babu dalili.
[4] Ka nuna mini hanyoyinka, ya Ubangiji, ka koya mini hanyoyinka;
[5] ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini, gama kai ne Allah Mai cetona, kuma begena yana a kanka dukan yini.
[6] Ka tuna, ya Ubangiji da jinƙai da kuma ƙaunarka mai girma, gama suna nan tun dā.
[7] Kada ka tuna da zunuban ƙuruciyata da kuma hanyoyin tawayena; bisa ga ƙaunarka ka tuna da ni, gama kai nagari ne, ya Ubangiji.
[8] Ubangiji nagari da mai adalci ne; saboda haka yakan koyar da masu zunubi a hanyoyinsa.
[9] Yakan bi da masu tawali’u cikin abin da yake daidai ya kuma koyar da su hanyoyinsa.
[10] Dukan hanyoyin Ubangiji ƙaunatattu ne da kuma aminci ga waɗanda suke kiyaye abin da alkawari ya bukaci.
[11] Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka gafarta laifina, ko da yake mai girma ne.
[12] To wane ne mai tsoron Ubangiji? Zai koyar da shi a hanyar da ya zaɓa masa.
[13] Zai ci kwanakinsa a wadace, kuma zuriyarsa za su gāji ƙasar.
[14] Ubangiji yakan amince da waɗanda suke tsoronsa; yakan sa su san alkawarinsa.
[15] Idanuna kullum suna a kan Ubangiji, gama shi ne kaɗai zai kuɓutar da ƙafafuna daga tarko.
[16] Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai, gama na kaɗaice ina kuma wahala.
[17] Damuwoyin zuciyata sun ninka; ka ’yantar da ni daga wahalata.
[18] Ka dubi wahalata da kuma azabata ka ɗauke mini dukan zunubaina.
[19] Dubi yadda abokan gābana sun ƙaru da kuma yadda suka ƙara ƙina!
[20] Ka tsare raina ka kuma kuɓutar da ni; kada ka bari in sha kunya, gama na nemi mafaka daga gare ka.
[21] Bari mutunci da adalci su tsare ni, domin begena yana a kanka.
[22] Ka fanshi Isra’ila, ya Allah, daga dukan wahalarsu!