[1] Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
[2] Bari Isra’ila yă ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
[3] Bari gidan Haruna yă ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
[4] Bari waɗanda suke tsoron Ubangiji su ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
[5] Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji, ya kuwa amsa ta wurin ’yantar da ni.
[6] Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai yi mini?
[7] Ubangiji yana tare da ni; shi ne mai taimakona. Zan yi nasara a kan abokan gābana.
[8] Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga mutum.
[9] Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga sarakuna.
[10] Dukan al’ummai sun kewaye ni, amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.
[11] Sun kewaye ni a kowane gefe, amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.
[12] Sun rufe ni kamar ƙudan zuma, amma suka mutu nan da nan kamar ƙayayyuwa masu cin wuta; a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.
[13] An ture ni baya na kusa fāɗuwa, amma Ubangiji ya taimake ni.
[14] Ubangiji ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona.
[15] Sowa ta farin ciki da nasara sun fito a cikin tentunan adalai, “Hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa!
[16] An ɗaga hannun dama na Ubangiji sama; hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa!”
[17] Ba zan mutu ba amma zan rayu, zan kuwa yi shelar abin da Ubangiji ya yi.
[18] Ubangiji ya hore ni sosai, amma bai ba da ni ga mutuwa ba.
[19] Buɗe mini ƙofofin adalci; zan shiga in kuma yi godiya ga Ubangiji.
[20] Wannan ne ƙofar Ubangiji inda adalai za su shiga.
[21] Zan yi maka godiya, domin ka amsa mini; ka zama mai cetona.
[22] Zabura Dutsen da magina suka ƙi ya zama mai amfani;
[23] Ubangiji ne ya yi haka, kuma abu mai daraja ne a idanunmu.
[24] Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi; bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.
[25] Ya Ubangiji, ka cece mu; Ya Ubangiji, ka ba mu nasara.
[26] Mai albarka ne shi mai zuwa cikin sunan Ubangiji. Daga gidan Ubangiji muna sa muku albarka.
[27] Ubangiji shi ne Allah ya kuma sa haskensa ya haskaka a kanmu. Da kwanoni a hannunmu, muka shiga jerin gwanon biki ku kai su ƙahoni na bagade.
[28] Kai ne Allahna, zan kuwa yi maka godiya; kai ne Allahna, zan kuwa ɗaukaka ka.
[29] Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.