[1] Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya! Ka kafa ɗaukakarka bisa sammai.
[2] Daga leɓunan yara da jarirai ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka da masu ɗaukan fansa su yi shiru.
[3] Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu,
[4] wane ne mutum da kake tunawa da shi, ɗan mutum da kake lura da shi?
[5] Ka yi shi ƙasa kaɗan da Allah ka yi masa rawani da ɗaukaka da girma.
[6] Ka mai da shi mai mulki bisa ayyukan hannuwanka; ka sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa,
[7] dukan shanu da tumaki, da kuma namun jeji,
[8] tsuntsayen sararin sama da kifin teku, da dukan abin da yake yawo a ƙarƙashin ruwan teku.
[9] Ya Ubangiji, shugabanmu, sunanka da girma take a cikin dukan duniya!