Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:52

[1] Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi. Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[2] Ku yi godiya ga Allahn alloli. Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[3] Ku yi godiya ga Ubangijin iyayengiji. Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[4] Gare shi wanda shi kaɗai yake aikata abubuwan banmamaki, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[5] Wanda ta wurin ganewarsa ya yi sammai, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[6] Wanda ya shimfiɗa duniya a kan ruwaye, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[7] Wanda ya yi manyan haskoki, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[8] Rana don tă yi mulkin yini, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[9] Wata da taurari kuma don su yi mulkin dare; Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[10] Gare shi wanda ya kashe ’ya’yan fari Masar Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[11] Ya kuma fitar da Isra’ila daga cikinsu Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[12] Da hannu mai ƙarfi da hannu mai iko; Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[13] Gare shi wanda ya raba Jan Teku biyu Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[14] Ya kawo Isra’ila ta tsakiyarsa, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[15] Amma ya share Fir’auna da mayaƙansa cikin Jan Teku; Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[16] Gare shi wanda ya bi da mutanensa cikin hamada, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[17] Wanda ya buge manyan sarakuna, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[18] Ya karkashe manyan sarakuna, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[19] Sihon sarkin Amoriyawa Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[20] Da kuma Og sarkin Bashan, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[21] Ya kuma ba da ƙasarsu gādo, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[22] Gādo ga bawansa Isra’ila; Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[23] Shi wanda ya tuna da mu cikin ƙasƙancinmu Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[24] Ya kuma ’yantar da mu daga abokan gābanmu, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[25] Wanda kuma ke ba da abinci ga kowace halitta. Ƙaunarsa madawwamiya ce.

[26] Ku yi godiya ga Allah na sama. Ƙaunarsa madawwamiya ce.

Zabura — Chapters