Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:02

[1] Ka ji mu, ya Makiyayin Isra’ila, kai da ka bishe Yusuf kamar garke. Kai da kake zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, ka haskaka

[2] a gaban Efraim, Benyamin da Manasse. Ka tā da ƙarfinka; ka zo ka cece mu.

[3] Ka mai da mu, ya Allah; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu.

[4] Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, har yaushe fushinka zai yi ta ƙuna a kan addu’o’in mutanenka?

[5] Ka ciyar da su da burodin hawaye; ka sa suka sha hawaye ta cikakken kwaf.

[6] Ka mai da mu abin faɗa ga maƙwabtanmu, kuma abokan gābanmu suna mana ba’a.

[7] Ka mai da mu, ya Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu za mu kuwa cetu.

[8] Ka fitar da inabi daga Masar; ka kori al’ummai ka kuma dasa shi.

[9] Ka gyara wuri saboda shi, ya kuwa yi saiwa ya cike ƙasa.

[10] Aka rufe duwatsu da inuwarsa, manya-manyan itatuwan al’ul da rassansa.

[11] Ya miƙe rassansa zuwa Teku tohonsa har zuwa Kogi.

[12] Me ya sa ka rurrushe bangayensa don duk masu wucewa su tsinke ’ya’yan inabinsa?

[13] Aladu daga kurmi suna ɓarnatar da shi halittun gonaki kuma suna cinsa.

[14] Ka komo wurinmu, ya Allah Maɗaukaki! Ka duba daga sama ka gani! Ka lura da wannan inabi,

[15] saiwar da hannun damarka ya dasa, ɗan da ka renar wa kanka.

[16] An yanke inabinka, an ƙone shi da wuta; a tsawatawarka mutanenka sun hallaka.

[17] Bari hannunka yă zauna a kan mutumin da yake hannun damarka, ɗan mutum da ka renar wa kanka.

[18] Ta haka ba za mu juye mu bar ka ba; ka rayar da mu, za mu kuwa kira bisa sunanka.

[19] Ka mai da mu, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu.

Zabura — Chapters