Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:19

[1] Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi; Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala.

[2] Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa; zai albarkace shi a cikin ƙasar ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba.

[3] Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi.

[4] Na ce, “Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai; ka warkar da ni, gama na yi maka zunubi.”

[5] Abokan gābana suna muguwar magana a kaina cewa, “Yaushe zai mutu sunansa yă ɓace ne?”

[6] Duk sa’ad da wani ya zo ganina, yakan yi maganar ƙarya, yayinda zuciyarsa tana tattare da cin zarafi; sa’an nan yă fita yă yi ta bazawa ko’ina.

[7] Dukan abokan gābana suna raɗa tare a kaina; suna fata mugun abu ya same ni, suna cewa,

[8] “Mugun ciwo ya kama shi; ba zai taɓa tashi daga inda yake kwanciya ba.”

[9] Har abokina na kurkusa, wanda na amince da shi, wanda muke cin abinci tare, ya juya yana gāba da ni.

[10] Amma kai, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai, ka tā da ni, don in sāka musu.

[11] Na sani kana jin daɗina, gama abokin gābana ba zai ci nasara a kaina ba.

[12] Cikin mutuncina ka riƙe ni ka sa ni a gabanka har abada.

[13] Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, har abada abadin. Amin kuma Amin.

Zabura — Chapters