Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:12

[1] Na yi farin ciki tare da waɗanda suka ce da ni, “Bari mu tafi gidan Ubangiji.”

[2] Ƙafafunmu suna tsaye a ƙofofinki, ya Urushalima.

[3] An gina Urushalima kamar birnin da aka yi a harhaɗe wuri guda.

[4] A can ne kabilu suke haurawa, kabilan Ubangiji, don su yabi sunan Ubangiji bisa ga farillan da aka ba wa Isra’ila.

[5] A can kursiyoyin shari’a yake tsaye, kursiyoyin gidan Dawuda.

[6] Ku yi addu’a don salamar Urushalima, “Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya.

[7] Bari salama ta kasance a katangarki zaman lafiya kuma a fadodinki.”

[8] Saboda ’yan’uwana da kuma abokaina, zan ce, “Salama tă kasance tare da ke.”

[9] Saboda gidan Ubangiji Allahnmu, zan nemi wadatarki.

Zabura — Chapters