Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:16

[1] Allah yana shugabanta cikin babban taro; yakan zartar da hukunci a cikin “alloli”.

[2] “Har yaushe za ku kāre marasa adalci ku kuma goyi bayan mugaye? Sela

[3] Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.

[4] Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.

[5] “Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba. Suna yawo cikin duhu; an girgiza dukan tussan duniya.

[6] “Na ce, ‘Ku “alloli” ne; dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne.

[7] Amma za ku mutu kamar mutum kurum; za ku fāɗi kamar duk wani mai mulki.”

[8] Ka tashi, ya Allah, ka shari’anta duniya, gama dukan al’ummai gādonka ne.

Zabura — Chapters