Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:18

[1] Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; bari kukata ta neman taimako ta zo gare ka.

[2] Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni sa’ad da nake cikin damuwa. Ka juye kunnenka gare ni; sa’ad da na yi kira, ka amsa mini da sauri.

[3] Gama kwanakina sun ɓace kamar hayaƙi; ƙasusuwana suna ƙuna kamar jan wuta.

[4] Zuciyata ta kamu da ciwo ta kuma bushe kamar ciyawa; na manta in ci abinci.

[5] Saboda nishina mai ƙarfi na rame na bar ƙasusuwa kawai.

[6] Ni kamar mujiyar jeji ne, kamar mujiya a kufai.

[7] Na kwanta a faɗake; na zama kamar tsuntsun da yake shi kaɗai a kan rufin ɗaki.

[8] Dukan yini abokan gābana suna tsokanata; waɗanda suke mini ba’a suna amfani da sunana yă zama abin la’ana.

[9] Gama ina cin toka a matsayin abincina ina kuma gauraye abin sha nawa da hawaye

[10] saboda fushinka mai girma, gama ka ɗaga ni sama ka yar a gefe.

[11] Kwanakina suna kamar inuwar yamma; na bushe kamar ciyawa.

[12] Amma kai, ya Ubangiji, kana zaune a kursiyinka har abada; sunan da ka yi zai dawwama a dukan zamanai.

[13] Za ka tashi ka kuma ji tausayin Sihiyona, gama lokaci ne na nuna alheri gare ta; ƙayyadadden lokacin ya zo.

[14] Gama duwatsunta suna da daraja ga bayinka; ƙurarta kawai kan sa su ji tausayi.

[15] Al’ummai za su ji tsoron sunan Ubangiji, dukan sarakunan duniya za su girmama ɗaukakarka.

[16] Gama Ubangiji zai sāke gina Sihiyona ya kuma bayyana a ɗaukakarsa.

[17] Zai amsa addu’ar marasa ƙarfi; ba zai ƙyale roƙonsu ba.

[18] Bari a rubuta wannan don tsara mai zuwa, cewa mutanen da ba a riga an halitta ba za su yabi Ubangiji,

[19] “Ubangiji ya duba ƙasa daga wurinsa mai tsarki a bisa, daga sama ya hangi duniya,

[20] don yă ji nishe-nishen ’yan kurkuku yă kuma saki waɗanda aka yanke musu hukuncin mutuwa.”

[21] Saboda haka za a furta sunan Ubangiji a Sihiyona yabonsa kuma a Urushalima

[22] sa’ad da mutane da mulkoki suka tattaru don su yi wa Ubangiji sujada.

[23] Cikin rayuwata, ya karye ƙarfina; ya gajartar da kwanakina.

[24] Sai na ce, “Kada ka ɗauke ni a tsakiyar kwanakina, ya Allah; shekarunka suna bi cikin dukan zamanai.

[25] A farkon fari ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne.

[26] Za su hallaka, amma za ka ci gaba; duk za su tsufe kamar riga. Kamar riga za ka canja su za a kuwa zubar da su.

[27] Amma kana nan yadda kake, kuma shekarunka ba za su taɓa ƙarewa ba.

[28] ’Ya’yan bayinka za su zauna a gabanka; zuriyarsu za su kahu a gabanka.”

Zabura — Chapters