Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:06

[1] Na yi kira gare ka, ya Ubangiji; ka zo da sauri. Ka ji muryata sa’ad da na yi kira.

[2] Bari a sa addu’ata a gabanka kamar turaren ƙonawa; bari ɗagawa hannuwana ta zama kamar hadayar yamma.

[3] Ka sa mai tsaro a bakina, ya Ubangiji; ka yi tsaron ƙofar leɓunana.

[4] Kada ka bar zuciyata ta juya ga yin abin da yake mugu, ta sa kai ga aikata mugayen ayyuka tare da mutane masu aikata mugunta; kada ka bari in ci abincinsu.

[5] Bari mutum mai adalci yă buge ni, alheri ne; bar shi yă tsawata mini, mai ne a kaina. Kaina ba zai ƙi shi ba, duk da haka addu’ata kullum tana gāba da mugayen ayyuka.

[6] Za a jefar da masu mulkinsu ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, mugaye kuwa za su san cewa maganata daidai ne.

[7] Za su ce, “Kamar yadda mutum kan yi huda yă tsage ƙasa, haka aka watsar da ƙasusuwanmu a bakin kabari.”

[8] Amma na kafa idanuna a kanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka; a cikinka ina neman mafaka, kada ka miƙa ni ga mutuwa.

[9] Ka kiyaye ni daga tarkon da aka sa mini, daga tarkon da mugaye suka sa.

[10] Bari mugaye su fāɗa a cikin ragarsu, amma bari ni in zo in wuce lafiya.

Zabura — Chapters