Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:41

[1] Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji, ya raina.

[2] Zan yabi Ubangiji dukan kwanakina; zan rera yabo ga Allahna muddin raina.

[3] Kada ka sa zuciyarka ga sarakuna, ga mutane masu mutuwa, waɗanda ba sa iya ceto.

[4] Sa’ad da numfashinsu ya rabu da su sai su koma ƙasa; a wannan rana shirye-shiryensu sun zama banza.

[5] Mai albarka ne wanda Allah na Yaƙub ne taimakonsa, wanda sa zuciyarsa yana a kan Ubangiji Allahnsa.

[6] Mahaliccin sama da ƙasa, teku, da kome da yake cikinsu, Ubangiji, wanda yake mai aminci har abada.

[7] Yakan biya bukatun mutanen da aka danne ya kuma ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji yakan ’yantar da ’yan kurkuku,

[8] Ubangiji yakan ba wa makafi ido, Ubangiji yakan ɗaga waɗanda aka rusunar da su ƙasa, Ubangiji yana ƙaunar masu adalci.

[9] Ubangiji yana tsaron baƙi yana kuma lura da marayu da kuma gwauruwa, amma yakan lalatar da hanyoyin mugaye.

[10] Ubangiji yana mulki har abada, Allahnki, ya Sihiyona, daga zamani zuwa zamani. Yabi Ubangiji.

Zabura — Chapters