Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:20

[1] A wurin Ubangiji ne nake samun mafaka. Yaya za ku ce mini, “Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu.

[2] Gama duba, mugaye sun tanƙware bakkunansu; sun kuma ɗana kibiyoyinsu don su harbi mutanen kirki a zuciya daga cikin duhu.

[3] Sa’ad da aka tumɓuke tushe, me adali zai iya yi?”

[4] Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki; Ubangiji yana a kursiyinsa a sama. Yana kallon ’ya’yan mutane; idanunsa suna bincike su.

[5] Ubangiji yana bincike adalai, amma ransa yana ƙi mugaye da masu son rikici.

[6] A kan mugaye zai zuba garwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu; iska mai zafi zai zama rabonsu.

[7] Gama Ubangiji mai adalci ne, yana ƙaunar gaskiya masu adalci za su ga fuskarsa.

Zabura — Chapters