Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:57

[1] Ubangiji ne haskena da cetona, wa zan ji tsoro? Ubangiji ne mafakar raina, wane ne zan ji tsoro?

[2] Sa’ad da mugaye suka tasar mini don su cinye ni, sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari, sun yi tuntuɓe suka fāɗi.

[3] Ko da yake mayaƙa sun kewaye ni, zuciyata ba za tă ji tsoro ba; ko da yake ya ɓarke a kaina, duk da haka zan ƙarfafa.

[4] Abu guda na roƙi Ubangiji, wannan shi ne na nema, cewa in zauna a gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, in dubi kyan Ubangiji in kuma neme shi a cikin haikalinsa.

[5] Gama a lokacin wahala, zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa; zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa ya kuma sa ni can a bisa dutse.

[6] Sa’an nan kaina zai ɗaukaka a bisa abokan gābana waɗanda suka kewaye ni; a tabanakul nasa zan miƙa hadaya da sowa ta farin ciki; zan rera in kuma yi kiɗi ga Ubangiji.

[7] Ka ji muryata sa’ad da na yi kira, ya Ubangiji; ka yi mini jinƙai ka kuma amsa mini.

[8] Zuciyata kan faɗa game da kai, “Nemi fuskarsa!” Fuskarka, Ubangiji, zan nema.

[9] Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni, kada ka kore bawanka daga gare ka cikin fushi; kai ne ka kasance mai taimakona. Kada ka ƙi ni ko ka yashe ni, Ya Allah Mai cetona.

[10] Ko da mahaifina da mahaifiyata sun yashe ni, Ubangiji zai karɓe ni.

[11] Ka koya mini hanyarka, ya Ubangiji; ka bi da ni a miƙaƙƙiyar hanya saboda masu danne ni.

[12] Kada ka ba da ni da sha’awar maƙiyina, gama masu shaidar ƙarya sun taso a kaina, suna numfasa tashin hankali.

[13] Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewa zan ga alherin Ubangiji; a ƙasar masu rai.

[14] Ka dogara ga Ubangiji, ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya ka kuma dogara ga Ubangiji.

Zabura — Chapters