Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:33

[1] Ina misalin kyan wurin zamanka, Ya Ubangiji Maɗaukaki!

[2] Raina yana marmari, har yana suma, don filayen gidan Ubangiji; zuciyata da namana na tā da murya domin Allah mai rai.

[3] Har tsada ma ta sami gida, tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa, inda za tă ƙyanƙyashe ’ya’yanta, wuri kusa da bagadenka, Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna.

[4] Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka; kullum suna ta yabonka. Sela

[5] Masu albarka ne waɗanda ƙarfinsu yana daga gare ka, waɗanda suka kafa zukatansu a yin tafiya zuwa wuri mai tsarki ne.

[6] Yayinda suke wuce ta Kwarin Baka, sukan mai da shi wurin maɓulɓulai; ruwan sama na farko kuma kan rufe shi da tafkuna.

[7] Suna ta ƙara ƙarfi, har sai kowanne ya bayyana a gaban Allah a Sihiyona.

[8] Ka ji addu’ata, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka saurare ni, ya Allah na Yaƙub. Sela

[9] Ka dubi garkuwarmu, ya Allah; ka duba da alheri a kan shafaffenka.

[10] Rana guda a filayen gidan sun fi dubu a wani wuri dabam; zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna da in zauna a tentunan mugaye.

[11] Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa; Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja; ba ya hana kowane abu mai kyau wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.

[12] Ya Ubangiji Maɗaukaki, mai albarka ne mutumin da ya dogara gare ka.

Zabura — Chapters