[1] Ina ƙaunar Ubangiji, gama ya ji muryata; ya ji kukata ta neman jinƙai.
[2] Domin ya juye kunnensa gare ni, zan kira gare shi muddin ina da rai.
[3] Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni, wahalar kabari sun zo a kaina; na cika da wahala da ɓacin rai.
[4] Sai na kira ga sunan Ubangiji na ce, “Ya Ubangiji, ka cece ni!”
[5] Ubangiji mai alheri ne da kuma mai adalci; Allahnmu yana cike da tausayi.
[6] Ubangiji yana tsare masu tawali’u; sa’ad da nake cikin tsananin bukata, ya cece ni.
[7] Ka kwantar da hankali, ya raina, gama Ubangiji mai alheri ne a gare ka.
[8] Gama kai, ya Ubangiji, ka ceci raina daga mutuwa, idanuna daga hawaye, ƙafafuna daga tuntuɓe,
[9] don in iya tafiya a gaban Ubangiji a ƙasar masu rai.
[10] Na gaskata, saboda haka na ce, “An azabtar da ni ƙwarai.”
[11] Kuma cikin rikicewana na ce, “Dukan mutane maƙaryata ne.”
[12] Yaya zan sāka wa Ubangiji saboda dukan alherinsa gare ni?
[13] Zan daga kwaf na ceto in kuma kira ga sunan Ubangiji.
[14] Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa.
[15] Abu mai daraja a gaban Ubangiji shi ne mutuwar tsarkakansa.
[16] Ya Ubangiji, da gaske ni bawanka ne; ni bawanka ne, ɗan baiwarka; ka ’yantar da ni daga sarƙoƙi.
[17] Zan yi hadayar godiya gare ka in kuma kira bisa sunan Ubangiji.
[18] Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa,
[19] a filayen gidan Ubangiji, a tsakiyarki, ya Urushalima. Yabi Ubangiji.