[1] Yabi Ubangiji. Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu, abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi!
[2] Ubangiji ya gina Urushalima; ya tattara kamammu na Isra’ilan da aka kai bauta.
[3] Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu.
[4] Ya lissafta yawan taurari ya kuma kira kowannensu da suna.
[5] Shugabanmu mai girma ne mai iko duka; ganewarsa ba shi da iyaka.
[6] Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai yakan yar da mugaye a ƙasa.
[7] Rera wa Ubangiji waƙar godiya; ku kada garaya ga Allahnmu.
[8] Ya rufe sararin sama da gizagizai; yana tanada wa duniya ruwan sama yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai.
[9] Yakan tanada wa shanu abinci da kuma saboda ’ya’yan hankaki sa’ad da suka yi kira.
[10] Jin daɗinsa ba ya a ƙarfin doki, balle farin cikinsa yă kasance a ƙafafun mutum;
[11] Ubangiji yakan yi farin ciki a waɗanda suke tsoronsa, waɗanda suke sa zuciya a ƙaunarsa marar ƙarewa.
[12] Ki ɗaukaka Ubangiji, ya Urushalima; ki yabi Allahnki, ya Sihiyona.
[13] Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinki yana kuma albarkace mutanenki a cikinki.
[14] Yana ba da salama ga iyakokinki yana kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.
[15] Yana ba da umarninsa ga duniya; maganarsa tana tafiya da sauri.
[16] Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar ulu yă kuma watsar da hazo kamar toka.
[17] Yana zuba ƙanƙara kamar ƙananan duwatsu. Wa zai iya jure wa sanyin da ya aiko?
[18] Yakan aiki maganarsa ta kuwa narkar da su; yakan tā da iskarsa, ruwaye kuwa su gudu.
[19] Ya bayyana maganarsa ga Yaƙub, dokokinsa da ƙa’idodinsa ga Isra’ila.
[20] Bai yi wannan ga wata al’umma ba; ba su san dokokinsa ba. Yabi Ubangiji.