[1] Ku ji wannan, dukanku mutane; ku saurara, dukanku waɗanda suke zama a wannan duniya,
[2] babba da yaro mai arziki da talaka.
[3] Bakina zai yi maganar hikima; magana daga zuciyata za tă ba da ganewa.
[4] Zan juye kunnena ga karin magana; da garaya zan ƙarfafa kacici-kacicina.
[5] Don me zan ji tsoro sa’ad da mugayen kwanaki suka zo, sa’ad da mugaye masu ruɗu suka kewaye ni,
[6] waɗanda suka dogara ga arzikinsu suna kuma fariya a kan yawan arzikinsu?
[7] Ba wani da zai iya ceton ran wani ko yă ba wa Allah kuɗin fansa saboda shi,
[8] kuɗin fansa domin rai yana da tsada, babu abin da za a biya da ya taɓa isa,
[9] da zai sa yă ci gaba da rayuwa har abada yă hana shi shigan kabari yă ruɓa.
[10] Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa; wawaye da marasa azanci su ma kan hallaka su bar wa waɗansu arzikinsu.
[11] Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada, Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa, ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu.
[12] Amma mutum, kome arzikinsa, ba ya dawwama; shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.
[13] Wannan ne ƙaddarar waɗanda suke dogara a kansu, da kuma ta mabiyansu, waɗanda suka tabbatar da faɗinsu. Sela
[14] Kamar tumaki an ƙaddara su ga kabari; za su kuwa zama abincin mutuwa amma masu gaskiya za su yi mulki a kansu da safe. Kamanninsu za su ruɓe a cikin kabari, nesa da gidajensu masu tsada.
[15] Amma Allah zai ceci raina daga kabari; tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa. Sela
[16] Kada ka razana da yawa sa’ad da mutum ya yi arziki sa’ad da darajar gidansa ta ƙaru;
[17] gama ba zai ɗauki kome tare da shi sa’ad da ya mutu ba, darajarsa ba za tă gangara tare da shi ba.
[18] Ko da yake yayinda yake a raye ya ɗauka kansa mai albarka ne, mutane kuma sun yabe ka sa’ad da kake cin nasara,
[19] zai gamu da tsarar kakanninsa, waɗanda ba za su taɓa ganin hasken rayuwa ba.
[20] Mutumin da yake da arziki ba tare da ganewa ba shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.