Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:02

[1] Ubangiji yana mulki, yana sanye da ɗaukaka; Ubangiji yana sanye da ɗaukaka yana kuma sanye da ƙarfi. An kafa duniya daram; ba za a iya matsar da ita ba.

[2] An kafa kursiyin tun da daɗewa; kana nan tun fil azal.

[3] Tekuna sun taso, ya Ubangiji, tekuna sun ta da muryarsu; tekuna sun tā da ta raƙumansu masu tumbatsa.

[4] Mafi ƙarfi fiye da tsawan manyan ruwaye, mafi ƙarfi fiye da ikon raƙuman ruwan teku, Ubangiji mai zama a bisa mai girma ne.

[5] Ƙa’idodinka suna nan daram; tsarki ya yi wa gidanka ado har kwanaki marar ƙarewa, ya Ubangiji.

Zabura — Chapters