Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:55

[1] Maɗaukaki, Allah, Ubangiji, ya yi magana ya kuma kira duniya daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa.

[2] Daga Sihiyona, cikakkiya a kyau, Allah na haskakawa.

[3] Allahnmu yana zuwa ba kuwa zai yi shiru ba; wuta mai cinyewa a gabansa, babban hadari kuma ya kewaye shi.

[4] Ya kira sammai da suke bisa, da duniya, don yă shari’anta mutanensa.

[5] “Ku tattara mini shafaffuna, waɗanda suka yi alkawari da ni ta wurin hadaya.”

[6] Sammai kuwa sun yi shelar adalcinsa gama Allah kansa alƙali ne. Sela

[7] “Ku ji, ya mutanena, zan kuwa yi magana, Ya Isra’ila, zan kuwa ba da shaida a kanku. Ni ne Allah, Allahnku.

[8] Ba na tsawata muku saboda hadayunku ko kuwa hadayunku na ƙonawa, waɗanda kuka taɓa kawo a gabana.

[9] Ba na bukatan bijimi daga turkenku ko awaki daga garkunanku,

[10] gama kowace dabbar kurmi nawa ne, da kuma shanu a kan dubban tuddai.

[11] Na san kowane tsuntsun da yake a duwatsu kuma halittun filaye nawa ne.

[12] Da a ce ina jin yunwa ai, ba sai na faɗa muku ba, gama duniyar nawa ne, da kome da yake cikinta.

[13] Ina cin naman bijimai ne ko ina shan jinin awaki ne?

[14] “Ku miƙa hadayar godiya ga Allah, ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka,

[15] ku kira gare ni a ranar wahala; zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.”

[16] Amma ga mugaye, Allah ya ce, “Wace dama ce kuke da ita na haddace dokokina ko na yin maganar alkawarina a leɓunanku?

[17] Kun ƙi umarnina kuka kuma zubar da kalmomina a bayanku

[18] Sa’ad da kuka ga ɓarawo, kukan haɗa kai da shi; kukan haɗa kai da mazinata.

[19] Kuna amfani da bakunanku don mugunta kuna kuma gyara harshenku don ruɗu.

[20] Kuna ci gaba da magana a kan ɗan’uwanku ku kuma yi maganar ƙarya a kan ɗan mahaifinku.

[21] Kun yi waɗannan abubuwa na kuwa yi shiru; kun ɗauka gaba ɗaya ni kamar ku ne. Amma zan tsawata muku in kuma zarge ku a fuskarku.

[22] “Ku lura da wannan, ku da kuka manta da Allah, ko kuwa in yayyage ku kucu-kucu, ba kuma wanda zai cece ku.

[23] Shi wanda ya miƙa hadayun godiya yakan girmama ni, ya kuma shirya hanya saboda in nuna masa ceton Allah.”

Zabura — Chapters