[1] Ya Ubangiji, Allahn da yake ramuwa, Ya Allah wanda yake ramuwa, ka haskaka.
[2] Ka tashi, ya Alƙalin duniya; ka sāka wa masu girman kai abin da ya dace da su.
[3] Har yaushe mugaye, ya Ubangiji har yaushe mugaye za su yi ta murna?
[4] Suna ta yin maganganun fariya; dukan masu aikata mugunta sun cika da fariya.
[5] Suna murƙushe mutanenka, ya Ubangiji; suna danne gādonka.
[6] Suna kashe gwauraye da kuma baƙi; suna kisan marayu.
[7] Suna ce, “Ubangiji ba ya gani; Allah na Yaƙub bai kula ba.”
[8] Ku mai da hankali, ku marasa azanci a cikin mutane; ku wawaye, yaushe za ku zama masu hikima?
[9] Shi da ya sa kunne ba don a ji ba ne? Shi da ya yi ido ba don yă gani ba ne?
[10] Shi da yake yi wa al’ummai horo ba ya hukunci ne? Shi da yake koya wa mutum ba shi da sani ne?
[11] Ubangiji ya san tunanin mutum; ya san cewa tunaninsu banza ne.
[12] Mai albarka ne mutumin da ka yi masa horo, ya Ubangiji, mutumin da ka koyar daga dokarka;
[13] kana ba shi sauƙi a lokacin wahala, sai har an haƙa rami wa mugaye.
[14] Gama Ubangiji ba zai ƙi mutanensa ba; ba zai taɓa yashe gādonsa ba.
[15] Za a sāke kafa hukunci a kan adalci, kuma dukan masu adalci a zuciya za su bi shi.
[16] Wane ne zai yi gāba da mugaye domina? Wane ne zai ɗauki matsayi ya yi gāba da masu aikata mugunta domina?
[17] Da ba don Ubangiji ya yi mini taimako ba, da tuni na zauna shiru a wurin mutuwa.
[18] Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,” ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni.
[19] Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina, ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina.
[20] Zai yiwu kursiyin da ya cika da lalaci yă haɗa kai da kai, wanda yake kawo azaba ta wurin abin da ya zartar?
[21] Sun yi ƙungiya tare a kan mai adalci suka yanke wa marar laifi hukuncin mutuwa.
[22] Amma Ubangiji ya zama kagarata, Allahna kuma dutsen da nake samun mafaka.
[23] Zai sāka musu saboda zunubansu yă kuma hallaka su saboda muguntarsu; Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.