[1] Ka cece ni daga abokan gābana, ya Allah; ka tsare ni daga waɗanda suka tayar mini.
[2] Ka kuɓutar da ni daga masu aikata mugunta ka kuma cece ni daga masu kisa.
[3] Duba yadda suka kwanta suna jirana! Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da ni ba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji.
[4] Ban yi wani laifi ba, duk da haka suna a shirye su fāɗa mini. Tashi ka taimake ni; dubi halin da nake ciki!
[5] Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, ka tashi ka hukunta dukan al’ummai; kada ka nuna jinƙai ga mugaye maciya amana. Sela
[6] Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni.
[7] Dubi abin da suke tofawa daga bakunansu, suna tofar da takuba daga leɓunansu, suna cewa, “Wa zai ji mu?”
[8] Amma kai, ya Ubangiji, kakan yi musu dariya; kana yi wa dukan waɗannan al’ummai ba’a.
[9] Ya ƙarfina, na dogara gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata,
[10] Allah mai ƙaunata. Allah zai sha gabana zai kuma sa in yi dariya a kan waɗanda suke magana marar kyau a kaina.
[11] Amma kada ka kashe su, ya Ubangiji garkuwarmu, in ba haka mutanena za su manta. Cikin ikonka ka sa su yi ta yawo barkatai, ka kuma kawar da su.
[12] Saboda zunuban bakunansu, saboda maganganun leɓunansu, bari a kama su cikin fariyarsu. Saboda zage-zage da ƙarairayin da suke yi,
[13] ka cinye su da hasala, ka cinye su sarai. Sa’an nan za a sani a iyakar duniya cewa Allah yana mulki a bisa Yaƙub. Sela
[14] Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni.
[15] Suna ta yawo neman abinci su kuwa yi haushi in ba su ƙoshi ba.
[16] Amma zan rera game da ƙarfinka, da safe zan rera game da ƙaunarka; gama kai ne mafakata, kagarata a lokacin wahala.
[17] Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata, Allah mai ƙaunata.