Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:37

[1] Zan rera wa ƙauna da adalcinka; gare ka, ya Ubangiji, zan rera yabo.

[2] Zan yi hankali ga yin rayuwa marar zargi, yaushe za ka zo gare ni? Zan bi da sha’anin gidana da zuciya marar abin zargi

[3] Ba zan kafa a gaban idanuna 1 wani abu marar kyau ba. Na ƙi jinin ayyukan mutane marasa aminci; ba za su manne mini ba.

[4] Mutane masu mugun zuciya za su nesa da ni; ba abin da zai haɗa ni da mugunta.

[5] Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye shi za a kashe; duk mai renin wayo da mai girman kai, ba zan jure masa ba.

[6] Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar, don su zauna tare da ni; tafiyarsa ba ta da zargi zai yi mini hidima.

[7] Babu mai ruɗun da zai zauna a gidana; babu mai ƙaryan da zai tsaya a gabana.

[8] Kowace safiya zan rufe bakunan dukan mugaye a ƙasar; zan yanke kowane mai aikata mugunta daga birnin Ubangiji.

Zabura — Chapters