[1] Ya Allah, kada ka yi shiru; kada ka tsaya cik, ya Allah, kada ka daina motsi.
[2] Dubi yadda abokan gābanka suke fariya, dubi yadda maƙiyanka suke ɗaga kansu.
[3] Da wayo suna ƙulle-ƙulle a kan mutanenka; suna shirya maƙarƙashiya a kan waɗanda kake so.
[4] Suna cewa, “Ku zo, bari mu hallaka su ɗungum a matsayin al’umma, don kada a ƙara tuna da sunan Isra’ila.”
[5] Da zuciya ɗaya suka yi ƙulle-ƙulle tare; suka haɗa kai gāba da kai,
[6] tentunan Edom da na mutanen Ishmayel, na Mowab da kuma na Hagirawa,
[7] Gebal, Ammon da Amalek, Filistiya, tare da mutanen Taya.
[8] Har Assuriya ma ta haɗa kai da su don ta ba da ƙarfi ga zuriyar Lot. Sela
[9] Ka yi musu abin da ka yi wa Midiyan, yadda ka yi wa Sisera da Yabin a kogin Kishon,
[10] waɗanda suka hallaka a En Dor suka zama kamar juji a ƙasa.
[11] Ka mai da manyansu kamar Oreb da Zeyib, dukan sarakunansu kamar Zeba da Zalmunna,
[12] waɗanda suka ce, “Bari mu mallaki wuraren kiwon Allah.”
[13] Ka mai da su kamar ɗan tsiron da kan karye, iska ta yi ta turawa, ya Allahna, kamar yayin da iska take hurawa,
[14] kamar yadda wuta ke cin kurmi ko harshen wutar da take ci a kan duwatsu,
[15] haka za ka kore su da iska mai ƙarfi ka kuma firgita su da guguwarka.
[16] Ka rushe fuskokinsu da kunya don mutane su nemi sunanka, ya Ubangiji.
[17] Bari su kasance cikin kunya da taƙaici; bari su hallaka cikin wulaƙanci.
[18] Bari su san cewa kai, wanda sunansa ne Ubangiji, cewa kai kaɗai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya.