Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:51

[1] Ya Ubangiji Allahna, na zo neman mafaka a wurinka; ka cece ni ka kuɓutar da ni daga dukan waɗanda suke bi na,

[2] in ba haka ba za su yayyage ni kamar zaki su ɓarke ni kucu-kucu ba tare da wani da zai cece ni ba.

[3] Ya Ubangiji Allahna, in na yi kuskure aka kuwa sami laifi a hannuwana,

[4] in na yi mugunta ga wanda yake zaman lafiya da ni ko kuwa ba da wani dalilin cuci abokin gābana,

[5] to, bari abokin gābana yă bi yă kuma cim mini; bari yă tattake raina a ƙasa ya sa in kwana a ƙura. Sela

[6] Ka tashi, ya Ubangiji, cikin fushinka; ka tashi gāba da fushin abokan gābana. Ka farka, Allahna, ka umarta adalci.

[7] Bari taron mutane su taru kewaye da kai. Ka yi mulki a bisansu daga bisa;

[8] bari Ubangiji mai shari’ar mutane. Ka shari’anta ni Ya Ubangiji, bisa ga adalcina, bisa ga mutuncina, ya Mafi Ɗaukaka.

[9] Ya Allah mai adalci, wanda yake binciken tunani da zukata, ka kawo ƙarshen rikicin mugaye ka kuma sa adalai su zauna lafiya.

[10] Garkuwata shi ne Allah Mafi Ɗaukaka, wanda yake ceton masu tsabtar zuciya.

[11] Allah alƙali ne mai adalci, Allahn da yakan bayyana fushinsa kowace rana.

[12] In mutum bai tuba ba, Allah zai wasa takobinsa; zai tanƙware yă kuma ɗaura bakansa.

[13] Ya shirya makamansa masu dafi; ya shirya kibiyoyinsa masu wuta.

[14] Wanda yake da cikin mugunta ya kuma ɗauki cikin damuwa yakan haifi ƙarya.

[15] Wanda ya haƙa rami yakan fāɗa cikin ramin da ya haƙa.

[16] Damuwar da ya ja yakan sāke nannaɗe a kansa; fitinarsa takan sauka a kansa.

[17] Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa zan kuma rera yabo ga sunan Ubangiji Mafi Ɗaukaka.

Zabura — Chapters