Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:30

[1] Yabo ya dace da kai, ya Allah, a Sihiyona; a gare ka za mu cika alkawuranmu

[2] Ya kai wanda yake jin addu’a a gare ka dukan mutane za su zo.

[3] Sa’ad da zunubai suka sha ƙarfinmu, ka gafarta laifofinmu.

[4] Masu albarka ne waɗanda ka zaɓa ka kawo kusa don su zauna a filayenka! Mun cika da abubuwa masu kyau na gidanka, na haikalinka mai tsarki.

[5] Ka amsa mana da ayyuka masu banmamaki na adalci, Ya Allah Mai Cetonmu, begen dukan iyakar duniya da kuma na tekuna masu nesa,

[6] wanda ya yi duwatsu ta wurin ikonka, bayan ka kintsa kanka da ƙarfi,

[7] wanda ya kwantar da rurin tekuna, rurin raƙumansu, da kuma tumbatsar al’ummai.

[8] Waɗanda suke zama can da nesa sukan ji tsoron manyan ayyukanka; inda safe ke haskaka yamma kuma ta shuɗe kakan sa a yi waƙoƙin farin ciki.

[9] Kana kula da ƙasa kana kuma yi mata banruwa; kana azurta ta a yalwace. Rafuffukan Allah sun cika da ruwa don su ba mutane hatsi, don haka ne ka ƙaddara.

[10] Ka kwarara ta da ruwa ka kuma baje kunyoyinta; ka sa ta yi laushi da yayyafi ka kuma albarkaci tsire-tsirenta.

[11] Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka, amalankenka kuwa sun cika har suna zuba.

[12] Makiyayan hamada sun cika har suna zuba; tuddai sun rufu da murna.

[13] Wurin dausayin kiwo sun rufu da garkuna kwari kuma sun cika da hatsi; suna sowa don farin ciki.

Zabura — Chapters