Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 0:52

[1] Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya.

[2] Yi wa Ubangiji sujada da murna; ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.

[3] Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah. Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne; mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa.

[4] Ku shiga ƙofofinsa da godiya filayen gidansa kuma da yabo; ku gode masa ku kuma yabi sunansa.

[5] Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada; amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.

Zabura — Chapters