Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:13

[1] Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki; zan yabi sunanka har abada abadin.

[2] Kowace rana zan yabe ka in kuma ɗaukaka sunanka har abada abadin.

[3] Ubangiji da girma yake ya kuma cancanci yabo girmansa ya fi ƙarfin ganewar mutum.

[4] Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara; za su yi magana game da manyan ayyukanka.

[5] Za su yi zancen ɗaukakarka mai daraja, zan kuma yi tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.

[6] Za su yi magana game da ikon ayyukanka masu bantsoro, zan kuma yi shelar manyan ayyukanka.

[7] Za su yi bikin yalwar alherinka suka kuma rera adalcinka da farin ciki.

[8] Ubangiji mai alheri da kuma tausayi, mai jinkirin fushi cike kuma da ƙauna.

[9] Ubangiji nagari ne ga duka; yana tausayin dukan abubuwan da ya yi.

[10] Dukan abubuwan da ka yi za su yabe ka, ya Ubangiji; tsarkakanka za su ɗaukaka ka.

[11] Za su yi maganar ɗaukakar mulkinka za su kuma yi zancen ikonka,

[12] saboda dukan mutane su san manyan ayyukanka da ɗaukakar darajar mulkinka.

[13] Mulkinka madawwamin mulki ne, sarautarka kuma za tă dawwama cikin dukan zamanai. Ubangiji mai aminci ne ga dukan alkawuransa mai ƙauna kuma ga dukan abubuwan da ya yi.

[14] Ubangiji yana riƙe da dukan waɗanda suka faɗi yana kuma ɗaga dukan waɗanda aka rusunar da su ƙasa.

[15] Idanun kowa yana dogara gare ka, kana kuma ba su abincinsu a lokacin da ya dace.

[16] Ka buɗe hannunka ka kuma ƙosar da sha’awar kowane abu mai rai.

[17] Ubangiji mai adalci ne cikin dukan hanyoyinsa yana kuma nuna ƙauna ga dukan abubuwan da ya yi.

[18] Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi, ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.

[19] Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa; yakan ji kukansu yă kuma cece su.

[20] Ubangiji yakan lura da dukan waɗanda suke ƙaunarsa, amma dukan mugaye zai hallaka su.

[21] Bakina zai yi magana cikin yabon Ubangiji. Bari kowace halitta ta yabi sunansa mai tsarki har abada abadin.

Zabura — Chapters