Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 1:19

[1] Ka ji kukata, ya Allah; ka saurari addu’ata.

[2] Daga iyakar duniya na yi kira gare ka, na yi kira yayinda zuciyata ta karai; ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi.

[3] Gama kai ne mafakata, hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi.

[4] Ina marmari in zauna a tentinka har abada in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. Sela

[5] Gama ka ji alkawarina, ya Allah; ka ba ni gādo na waɗanda suke tsoron sunanka.

[6] Ka ƙara kwanakin ran sarki, shekarunsa su kasance a zamanai masu yawa.

[7] Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada; ka sa ƙaunarka da amincinka su tsare shi.

[8] Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunanka in kuma cika alkawarina kowace rana.

Zabura — Chapters