[1] Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
[2] Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata.
[3] Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki; bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.
[4] Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum.
[5] Ku tuna da abubuwan mamakin da ya yi, mu’ujizansa, da kuma hukunce-hukuncen da ya zartar,
[6] Ya ku zuriyar Ibrahim bawansa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub, zaɓaɓɓensa.
[7] Shi ne Ubangiji Allahnmu; kuma hukunce-hukuncensa suna a cikin dukan duniya.
[8] Yana tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu,
[9] alkawarin da ya yi da Ibrahim, rantsuwar da ya yi wa Ishaku.
[10] Ya tabbatar da shi ga Yaƙub a matsayin ƙa’ida, Isra’ila a matsayin madawwamin alkawari,
[11] “Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana a matsayin rabo za ka yi gādo.”
[12] Sa’ad da suke kima kawai, kima sosai, da kuma baƙi a cikinta,
[13] suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma, daga masarauta zuwa wata.
[14] Bai bar kowa yă danne su ba; saboda su, ya tsawata wa sarakuna,
[15] “Kada ku taɓa shafaffena; kada ku yi wa annabawa lahani.”
[16] Ya sauko da yunwa a kan ƙasa ya kuma lalace dukan tanadinsu na abinci;
[17] ya kuma aiki mutum a gabansu, Yusuf, da aka sayar a matsayin bawa.
[18] Suka raunana ƙafafunsa da sarƙa aka sa wuyansa cikin ƙarafa,
[19] sai abin da ya rigafaɗi ya cika sai da maganar Ubangiji ta tabbatar da shi mai gaskiya.
[20] Sarki ya aika aka kuma sake shi, mai mulkin mutane ya ’yantar da shi.
[21] Ya mai da shi shugaban gidansa, mai mulki a bisa dukan abin da ya mallaka,
[22] don yă umarci sarakunansa yadda ya ga dama yă kuma koya wa dattawa hikima.
[23] Sa’an nan Isra’ila ya shiga Masar; Yaƙub ya yi zama kamar baƙo a ƙasar Ham.
[24] Ubangiji ya mai da mutanensa suka yi ta haihuwa; ya sa suka yi yawa suka fi ƙarfin maƙiyansu,
[25] waɗanda ya juya zukatansu su ƙi mutanensa don su haɗa baki a kan bayinsa.
[26] Ya aiki Musa bawansa, da Haruna, wanda ya zaɓa.
[27] Suka yi mu’ujizansa a cikinsu, abubuwan mamakinsa a cikin ƙasar Ham.
[28] Ya aiko da duhu ya kuma sa ƙasar tă yi duhu, ba domin sun yi tawaye a kan maganarsa ba?
[29] Ya mai da ruwaye suka zama jini, ya sa kifayensu suka mutu.
[30] Ƙasarsu ta yi ta fid da kwaɗi, waɗanda suka haura cikin ɗakunan kwana na masu mulkinsu.
[31] Ya yi magana, sai tarin ƙudaje suka fito, cinnaku kuma ko’ina a ƙasar.
[32] Ya mai da ruwan samansu ya zama ƙanƙara, da walƙiya ko’ina a ƙasarsu;
[33] ya lalace inabinsu da itatuwan ɓaurensu ya ragargaza itatuwan ƙasarsu.
[34] Ya yi magana, sai fāri ɗango suka fito, fāran da ba su ƙidayuwa;
[35] suka cinye kowane abu mai ruwan kore a cikin ƙasarsu, suka cinye amfanin gonarsu
[36] Sa’an nan ya karkashe dukan ’yan fari a cikin ƙasarsu, nunan fari na dukan mazantakarsu.
[37] Ya fitar da Isra’ila, ɗauke da azurfa da zinariya, kuma daga cikin kabilansu babu wani da ya kāsa.
[38] Masar ta yi murna sa’ad da suka tafi, saboda tsoron Isra’ila ya fāɗo musu.
[39] Ya shimfiɗa girgije kamar mayafi, da kuma wuta don ta ba su haske da dare.
[40] Suka roƙa, ya kuwa ba su makware ya kuma ƙosar da su da abinci daga sama.
[41] Ya buɗe dutse, sai ruwa ya ɓulɓulo, kamar kogi ya gudu zuwa cikin hamada.
[42] Ya tuna da alkawarinsa mai tsarki da ya ba wa bawansa Ibrahim.
[43] Ya fitar da mutanensa da farin ciki, zaɓaɓɓunsa da sowa ta farin ciki;
[44] ya ba su ƙasashen al’ummai, suka kuma sami gādon abin da waɗansu sun sha wahala a kai,
[45] don su kiyaye farillansa su kuma kiyaye dokokinsa. Yabo ga Ubangiji.