Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:25

[1] Ka ji addu’ata, ya Allah, kada ka ƙyale roƙona;

[2] ka ji ni ka kuma amsa mini. Tunanina yana damuna na kuma gaji tilis

[3] hankalina ya tashi saboda yawan surutan masu ƙina, saboda danniyar mugaye. Gama sukan jawo mini wahala, suna jin haushina suna ƙina.

[4] Zuciyata tana wahala a cikina; tsorace-tsoracen mutuwa sun sha kaina.

[5] Tsoro da rawan jiki sun kama ni; razana ta sha kaina.

[6] Na ce, “Kash, da a ce ina da fikafikan kurciya mana! Ai, da na yi firiya na tafi na huta,

[7] da na tafi can da nisa na zauna a hamada; Sela

[8] da na hanzarta na tafi wurin mafakata, nesa da muguwar iska da hadiri.”

[9] Ka rikitar da mugaye, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu, gama na ga rikici da faɗa a cikin birni.

[10] Dare da rana suna yawo a kan katanga; mugun hali da zargi suna a cikinta.

[11] Rundunar hallaka suna aiki a cikin birni; barazana da ƙarairayi ba sa taɓa barin titunanta.

[12] Da a ce abokin gāba ne ke zagina, da na jure da shi; da a ce maƙiyi yana tā da kansa a kaina, da na ɓoye daga gare shi.

[13] Amma kai ne, mutum kamar ni, abokina, abokina na kurkusa,

[14] wanda na taɓa jin daɗin zumunci da shi sosai yayinda muke tafiya tare a taron jama’a a gidan Allah.

[15] Bari mutuwa ta ɗauki abokan gābana ba labari; bari su gangara da rai zuwa cikin kabari, gama mugunta tana samun masauƙi a cikinsu.

[16] Amma na kira ga Allah, Ubangiji kuwa ya cece ni.

[17] Safe, rana da yamma ina kuka da nishi, yakan kuwa ji muryata.

[18] Yakan fisshe ni lafiya daga yaƙin da ake yi da ni, ko da yake da yawa suna gāba da ni.

[19] Allah, yana mulki har abada, zai ji su yă kuma azabtar da su, Sela mutanen da ba sa taɓa canja hanyoyinsu kuma ba sa tsoron Allah.

[20] Abokina ya kai wa abokansa hari; ya tā da alkawarinsa.

[21] Maganarsa tana da laushi kamar man zaitun, duk da haka yaƙi yana a cikin zuciyarsa; kalmominsa sun fi mai sulɓi, duk da haka takuba ne zārarru.

[22] Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji zai kuwa riƙe ku; ba zai taɓa barin mai adalci yă fāɗi ba.

[23] Amma kai, ya Allah, za ka kawar da mugaye zuwa cikin ramin lalacewa; masu kisa da mutane masu ruɗu ba za su kai rabin kwanakin rayuwarsu ba. Amma ni dai, na dogara gare ka.

Zabura — Chapters