[1] Yabi Ubangiji. Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
[2] Wane ne zai furta manyan ayyukan Ubangiji ko yă furta cikakken yabonsa?
[3] Masu albarka ne waɗanda suke yin adalci, waɗanda kullum suke yin abin da yake daidai.
[4] Ka tuna da ni, ya Ubangiji, sa’ad da ka nuna alheri ga mutanenka, ka zo ka taimake ni sa’ad da ka cece su,
[5] don in ji daɗin nasarar zaɓaɓɓunka, don in sami rabo cikin farin cikin al’ummarka in kuma shiga gādonka cikin yin yabo.
[6] Mun yi zunubi, kamar yadda kakanninmu suka yi; mun yi ba daidai ba muka kuma aikata mugunta.
[7] Sa’ad da kakanninmu suke a Masar, ba su damu da mu’ujizanka ba; ba su tuna yawan alheranka ba, suka kuma yi tayarwa a teku, Jan Teku.
[8] Duk da haka ya cece su saboda sunansa, don yă sanar da ikonsa mai girma.
[9] Ya tsawata wa Jan Teku, ya kuwa bushe; ya bi da su ta cikin zurfafa sai ka ce a hamada.
[10] Ya cece su daga hannun maƙiyi; daga hannun abokin gāba ya fanshe su.
[11] Ruwaye suka rufe abokan gābansu; babu ko ɗaya da ya tsira.
[12] Sa’an nan suka gaskata alkawarinsa suka kuma rera yabonsa.
[13] Amma nan da nan suka manta abin da ya yi ba su kuwa jira shawararsa ba.
[14] A cikin hamada suka bar sha’awarsu ta mamaye su a ƙasar da babu kome suka gwada Allah.
[15] Sai ya ba su abin da suka roƙa, amma ya aika musu da muguwar cuta.
[16] A sansani suka ji kishin Musa da kuma Haruna, wanda Ubangiji ya keɓe.
[17] Ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan ta binne iyalin Abiram.
[18] Wuta ta ƙuno a cikin mabiyansu; harshen wuta ya cinye mugaye.
[19] A Horeb suka yi ɗan maraƙi suka yi wa gunkin zubi daga ƙarfe sujada.
[20] Suka sauke Ɗaukakarsu saboda siffar bijimi, wanda yake cin ciyawa.
[21] Suka manta da Allahn da ya cece su, wanda ya aikata manyan abubuwa a Masar,
[22] mu’ujizai a ƙasar Ham ayyukan banrazana a Jan Teku.
[23] Don haka ya ce zai hallaka su, amma Musa, zaɓaɓɓensa, ya yi godo a gabansa don yă kau da hasalarsa daga hallaka su.
[24] Sai suka rena ƙasa mai ni’ima; ba su gaskata alkawarinsa ba.
[25] Suka yi gunaguni a tentunansu ba su kuwa yi biyayya da Ubangiji ba.
[26] Saboda haka ya rantse musu ya kuma ɗaga hannu cewa zai sa su mutu a cikin hamada,
[27] ya sa zuriyarsu su mutu a cikin al’ummai ya kuma watsar da su cikin dukan ƙasashe.
[28] Suka haɗa kai da Ba’al-Feyor suka kuma ci hadayun da aka miƙa wa allolin da ba su da rai;
[29] suka tsokane Ubangiji ya yi fushi ta wurin mugayen ayyukansu, sai annoba ta ɓarke a cikinsu.
[30] Amma Finehas ya miƙe tsaye ya ɗauki mataki, sai annobar ta daina.
[31] An ayana masa wannan a matsayin adalci har zamanai marar matuƙa masu zuwa.
[32] A ruwan Meriba suka ba Ubangiji fushi, sai wahala ta zo wa Musa saboda su;
[33] saboda sun yi tayarwa a kan Ruhun Allah, har mugayen kalmomi suka fito daga leɓunan Musa.
[34] Ba su hallakar da mutanen yadda Ubangiji ya umarce su ba,
[35] amma suka yi cuɗanya da al’ummai suka ɗauki al’adunsu.
[36] Suka yi wa gumakansu sujada, waɗanda suka zama tarko gare su.
[37] Suka miƙa ’ya’yansu maza hadaya ’yan matansu kuma ga aljanu.
[38] Suka zub da jini marar laifi, jinin ’ya’yansu maza da mata, waɗanda suka miƙa hadaya ga gumakan Kan’ana, ƙasar kuwa ta ƙazantu ta wurin jininsu.
[39] Suka ƙazantar da kansu ta wurin abin da suka yi; ta wurin ayyukansu suka yi karuwanci.
[40] Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da mutanensa ya ji ƙyamar gādonsa.
[41] Ya miƙa su ga al’ummai, maƙiyansu kuma suka yi mulki a kansu.
[42] Abokan gābansu suka danne su suka sa su a ƙarƙashin ikonsu.
[43] Sau da yawa ya cece su, amma sun nace su yi tawaye suka kuma lalace cikin zunubinsu.
[44] Amma ya lura da wahalarsu sa’ad da ya ji kukansu;
[45] saboda su ya tuna da alkawarinsa kuma daga yawan ƙaunarsa ya ji tausayi.
[46] Ya sa aka ji tausayinsu a wurin dukan waɗanda suka kame su.
[47] Ka cece mu, Ubangiji Allahnmu, ka kuma tattara mu daga al’ummai, don mu yi wa sunanka mai tsarki godiya mu kuma ɗaukaka cikin yabonka.
[48] Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Bari dukan mutane su ce, “Amin!” Yabo ga Ubangiji.