Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:16

[1] Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka.

[2] Gama kibiyoyinka sun soke ni, hannunka kuma ya fāɗo a kaina.

[3] Saboda hasalarka babu lafiya a jikina; ƙasusuwana ba lafiya saboda zunubina.

[4] Laifofina sun mamaye ni kamar nauyin da ya sha ƙarfin ɗauka.

[5] Miyakuna sun ruɓe suna kuma wari saboda wawancina na zunubi.

[6] An tanƙware ni aka kuma ƙasƙantar da ni; dukan yini ina ta kuka.

[7] Bayana yana fama da zazzaɓi; babu lafiya a jikina.

[8] Na gaji sharkaf an kuma ragargaza ni; ina nishi da wahala a cikin zuciyata.

[9] Dukan bukatata tana a shimfiɗe a gabanka, ya Ubangiji; ajiyar zuciyata ba ta ɓoyuwa daga gare ka.

[10] Zuciyata na bugu, ƙarfina kuma ya ƙare, har ma haske ya rabu da idanuna.

[11] Abokaina da maƙwabtana sun guje ni saboda miyakuna; maƙwabtana ba sa zuwa kusa.

[12] Waɗanda suke neman raina sun sa tarkonsu, waɗanda suke so su cuce ni suna zance lalatar da ni; yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.

[13] Ni kamar kurma ne, wanda ba ya ji, kamar bebe, wanda ba ya iya buɗe bakinsa.

[14] Na zama kamar mutumin da ba ya ji, wanda bakinsa ba ya iya ba da amsa.

[15] Na dogara gare ka, ya Ubangiji; za ka amsa, ya Ubangiji Allahna.

[16] Gama na ce, “Kada ka bar su su yi farin ciki a kaina ko su yi kirari a kaina sa’ad da ƙafata ta yi santsi.”

[17] Gama ina gab da fāɗuwa, kuma cikin azaba nake kullum.

[18] Na furta laifina; na damu da zunubina.

[19] Da yawa ne masu gāba da ni da ƙarfi; waɗanda suke kina ba dalili sun yi yawa.

[20] Waɗanda suke sāka alherina da mugunta, suna cin zarafina sa’ad da nake bin abin da yake daidai.

[21] Ya Ubangiji, kada ka yashe ni; kada ka yi nesa da ni, ya Allahna.

[22] Zo da sauri ka taimake ni, Ya Ubangiji Mai Cetona.

Zabura — Chapters