Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:01

[1] Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji daga sammai, yabe shi a bisa sammai.

[2] Yabe shi, dukanku mala’ikunsa, yabe shi, dukanku rundunarsa na sama.

[3] Yabe shi, rana da wata, yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.

[4] Yabe shi, ku bisa sammai da kuma ku ruwan bisa sarari.

[5] Bari su yabi sunan Ubangiji, gama ya umarta aka kuwa halicce su.

[6] Ya sa su a wurarensu har abada abadin; ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba.

[7] Yabi Ubangiji daga duniya, ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku,

[8] walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai, hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa,

[9] ku duwatsu da dukan tuddai, itatuwa masu ’ya’ya da dukan al’ul,

[10] namun jeji da dukan dabbobin gida, ƙanana halittu da tsuntsaye masu firiya,

[11] sarakunan duniya da dukan al’ummai, ku sarakuna da dukan masu mulkin duniya,

[12] samari da ’yan mata, tsofaffi da yara.

[13] Bari su yabi sunan Ubangiji, gama sunansa ne kaɗai mafi ɗaukaka; darajarsa ta fi ƙarfin duniya da sammai.

[14] Ya tayar wa mutanensa ƙaho, yabon dukan tsarkakansa, na Isra’ila, mutanen da suke kurkusa da zuciyarsa. Yabi Ubangiji.

Zabura — Chapters