Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:39

[1] Ya Ubangiji, ka bincike ni ka kuwa san ni.

[2] Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi; ka san tunanina daga nesa.

[3] Ka san fitata da kuma kwanciyata; ka saba da dukan hanyoyina.

[4] Kafin in yi magana da harshena ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji.

[5] Ka kewaye ni, gaba da baya; ka sa hannunka a kaina.

[6] Irin wannan sanin game da ni ya fi ƙarfin magana, ya fi ƙarfi in gane.

[7] Ina zan tafi daga Ruhunka? Ina zan gudu in tafi daga gabanka?

[8] In na haura zuwa sammai, kana a can; in na yi gado a zurfafa, kana a can.

[9] In na tashi a fikafikan safiya, in na sauka a gefe mai nisa na teku,

[10] can ma hannunka zai bishe ni, hannunka na dama zai riƙe ni gam.

[11] In na ce, “Tabbatacce duhu zai ɓoye ni haske kuma zai zama dare kewaye da ni,”

[12] duhu ma ba zai zama duhu gare ka ba; dare zai haskaka kamar rana, gama duhu ya yi kamar haske gare ka.

[13] Gama ka halicci ciki-cikina; ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.

[14] Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki; ayyukanka suna da banmamaki, na san da haka sosai.

[15] Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba sa’ad da aka yi ni asirce. Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.

[16] Idanunka sun ga jikina marar fasali; dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka kafin ɗayansu yă kasance.

[17] Tunaninka suna da daraja gare ni, ya Allah! Yawansu ba su da iyaka!

[18] A ce zan iya ƙirgansu, za su fi yashin teku yawa. Sa’ad da na farka, ina nan tare da kai har yanzu.

[19] Da kawai za ka kashe mugaye, ya Allah! Ku rabu da ni, ku masu kisankai!

[20] Suna magana game da kai da mugun nufi; maƙiyanka suna ɗaukan sunanka a banza.

[21] Ba ina ƙin masu ƙinka ba, ya Ubangiji, ina kuma ƙyamar waɗanda suke tayar maka ba?

[22] Ba ni da wani abu da nake musu sai kiyaye kawai; na ɗauke su abokan gābana.

[23] Ka bincike ni, ya Allah ka kuma san zuciyata; ka gwada ni ka kuma san damuwata.

[24] Duba ko akwai wani laifi a cikina, ka bishe ni a madawwamiyar hanya.

Zabura — Chapters