[1] Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka.
[2] Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma; Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo.
[3] Raina yana cikin wahala. Har yaushe, ya Ubangiji, har yaushe?
[4] Ka juyo, ya Ubangiji, ka cece ni; ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka.
[5] Babu wanda yakan tuna da kai sa’ad da ya mutu. Wa ke yabonka daga kabari?
[6] Na gaji tiƙis daga nishi. Dukan dare na jiƙe gadona da kuka na jiƙe kujerata da hawaye.
[7] Idanuna sun rasa ƙarfi da baƙin ciki; sun rasa ƙarfi saboda dukan abokan gābana.
[8] Ku tafi daga gare ni, dukanku masu aikata mugunta, gama Ubangiji ya ji kukata.
[9] Ubangiji ya ji kukata saboda jinƙansa; Ubangiji ya karɓi addu’ata.
[10] Dukan abokan gābana za su sha kunya su kuma karaya; za su juya da kunya nan da nan.