[1] Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai; ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki.
[2] Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne, Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya!
[3] Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu, mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu.
[4] Ya zaɓar mana gādonmu, abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. Sela
[5] Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki, Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni.
[6] Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai; ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai.
[7] Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya; ku rera zabura ta yabo gare shi.
[8] Allah yana mulki a bisa al’ummai; Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki.
[9] Manyan mutanen al’ummai sun taru a matsayin mutanen Allah na Ibrahim, gama sarkunan duniya na Allah ne; ana ɗaukaka shi ƙwarai.