Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:17

[1] Yana da kyau a yabi Ubangiji a kuma yi kiɗi ga sunanka, ya Mafi Ɗaukaka,

[2] don a yi shelar ƙaunarka da safe amincinka kuma da dare,

[3] da kiɗin molo mai tsirkiya goma da kuma ƙarar garaya.

[4] Gama ka sa na yi murna ta wurin ayyukanka, ya Ubangiji; na rera don farin ciki saboda ayyukan hannuwanka.

[5] Ina misalin ayyukanka, ya Ubangiji, tunaninka da zurfi suke ƙwarai!

[6] Mutum marar azanci ba zai sani ba, wawa ba zai gane ba,

[7] cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka, za a hallaka su har abada.

[8] Amma kai, ya Ubangiji, za a ɗaukaka har abada.

[9] Gama tabbatacce abokan gābanka, ya Ubangiji, tabbatacce abokan gābanka za su hallaka; za a watsar da dukan masu aikata mugunta.

[10] Ka ɗaukaka ƙahona kamar na ɓauna; an zubo mai masu kyau a kaina.

[11] Idanuna sun ga fāɗuwar maƙiyana; kunnuwana sun ji kukan mugayen maƙiyana.

[12] Adalai za su haɓaka kamar itacen dabino, za su yi girma kama al’ul na Lebanon;

[13] da aka daddasa a gidan Ubangiji, za su haɓaka a filayen gidan Allahnmu.

[14] Za su ci gaba da ba da ’ya’ya a tsufansu, za su kasance ɗanye kuma kore shar,

[15] suna shela cewa, “Ubangiji adali ne; shi ne Dutsena, kuma babu mugunta a cikinsa.”

Zabura — Chapters