[1] Akwai magana a cikin zuciyata game da zunubin mugu. Babu tsoron Allah a idanunsa.
[2] Gama a idanunsa yana ganin kansa wani abu ne wanda ya sha ƙarfi a gane ko ya ƙi zunubinsa.
[3] Kalmomin bakinsa mugaye ne da kuma ruɗu; ya daina zama mai hikima da yin alheri.
[4] Ko a kan gadonsa ma yana shirya mugunta; yakan sa kansa ga aikata zunubi kuma ba ya ƙin abin da ba shi da kyau.
[5] Ƙaunarka, ya Ubangiji, kan kai sammai, amincinka har sararin sammai.
[6] Adalcinka yana kama da manyan duwatsu, hukuncinka kamar zurfi mai girma. Ya Ubangiji, kana lura da mutum da dabba.
[7] Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa! Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka.
[8] Suna biki a yalwar gidanka; kakan ba su sha daga rafin farin cikinka.
[9] Gama a gare ka akwai maɓulɓular rai cikin haskenka mukan ga haske.
[10] Ka ci gaba da ƙaunarka ga waɗanda suka san ka, adalcinka ga masu gaskiyar zuciya.
[11] Kada ka bari ƙafar mai girman kai yă fāɗa mini, ko hannun mugu ya kore ni.
[12] Dubi yadda masu aikata zunubi suka fāɗi, a zube, ba za su kuwa iya tashi ba!