[1] Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, gama ya yi abubuwa masu banmamaki; hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki sun yi masa aikin ceto.
[2] Ubangiji ya sanar da cetonsa ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai.
[3] Ya tuna da ƙaunarsa da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Allahnmu.
[4] Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya, ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi;
[5] ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya, da garaya da ƙarar rerawa,
[6] tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago, ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki.
[7] Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa, duniya da kuma kome da yake cikinta.
[8] Bari koguna su tafa hannuwansu, bari duwatsu su rera tare don farin ciki;
[9] bari su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa domin yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya da adalci mutane kuma cikin gaskiya.