[1] Ya Ubangiji, ka tuna da Dawuda da kuma dukan irin wuyan da ya jimre.
[2] Ya yi rantsuwa ga Ubangiji ya kuma yi alkawari ga Maɗaukaki na Yaƙub cewa,
[3] “Ba zan shiga gidana ko in kwanta a gado ba,
[4] ba zan ba wa idanuna barci ba, ba gyangyaɗi wa idanuna,
[5] sai na sami wuri wa Ubangiji, mazauni domin Maɗaukaki na Yaƙub.”
[6] Mun ji haka a Efrata, muka yi ƙaro da shi a filayen Ya’ar,,
[7] “Bari mu tafi wurin zamansa; bari mu yi sujada a wurin sa ƙafafunsa,
[8] ka tashi, ya Ubangiji, ka kuma zo wurin hutunka, kai da akwatin alkawarin ƙarfinka.
[9] Bari a suturta firistocinka da adalci; bari tsarkakanka su rera don farin ciki.”
[10] Saboda Dawuda bawanka, kada ka ƙi shafaffenka.
[11] Ubangiji ya rantse wa Dawuda tabbataccen rantsuwa cewa ba zai janye ba cewa, “Ɗaya daga cikin zuriyarka zan sa a kan kursiyinka,
[12] in ’ya’yanka maza za su kiyaye alkawari da farillan da na koya musu, to ’ya’yansu maza za su zauna a kan kursiyinka har abada abadin.”
[13] Gama Ubangiji ya zaɓi Sihiyona, ya so ta zama mazauninsa,
[14] “Wannan shi ne wurin hutuna har abada abadin; a nan zan zauna ina mulki gama ina son ta,
[15] zan albarkace ta da tanade-tanade masu yawa; matalautanta za su ƙoshi da abinci.
[16] Zan suturta firistocinta da ceto, tsarkakanta kuma kullum za su rera don farin ciki.
[17] “A nan zan sa ƙaho ya yi girma wa Dawuda in kuma kafa fitila saboda shafaffena.
[18] Zan suturta abokan gābansa da kunya, amma rawanin da yake a kansa zai yi ta walƙiya.”