[1] Yabi Ubangiji. Yabi sunan Ubangiji; yabe shi, ku bayin Ubangiji,
[2] ku waɗanda kuke hidima a gidan Ubangiji, cikin filayen gidan Allahnmu.
[3] Yabi Ubangiji, gama Ubangiji nagari ne; rera yabo ga sunansa, gama wannan yana da kyau.
[4] Gama Ubangiji ya zaɓi Yaƙub ya zama nasa, Isra’ila ya zama mallakarsa mai daraja.
[5] Na san cewa Ubangiji yana da girma, cewa shugabanmu ya fi dukan alloli girma.
[6] Ubangiji yana yin abin da ya ga dama, a sammai da kuma a duniya, cikin tekuna da kuma cikin dukan zurfafansu.
[7] Yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya; yakan aika da walƙiya tare da ruwan sama ya fito da iska daga ɗakunan ajiyarsa.
[8] Ya kashe ’ya’yan fari na Masar, ’ya’yan fari na mutane da na dabbobi.
[9] Ya aiko da alamu da abubuwan banmamaki a tsirkiyarku, ya Masar, a kan Fir’auna da kuma dukan bayinsa.
[10] Ya bugi al’ummai masu yawa ya kuma karkashe manyan sarakuna,
[11] Sihon sarkin Amoriyawa, Og sarkin Bashan da kuma dukan sarakunan Kan’ana,
[12] ya kuma ba da ƙasarsa kamar abin gādo, abin gādo ga mutanensa Isra’ila.
[13] Sunanka, ya Ubangiji, dawwammame ne har abada, sanin da aka yi maka, ya Ubangiji, yana nan cikin dukan zamanai.
[14] Gama Ubangiji zai nuna cewa mutanensa ba su da laifi ya kuma ji tausayin bayinsa.
[15] Gumakan al’ummai azurfa ne da zinariya, da hannuwan mutane suka yi.
[16] Suna da bakuna, amma ba sa magana, idanu, amma ba sa gani;
[17] suna da kunnuwa, amma ba sa ji, ba kuwa numfashi a bakunansu.
[18] Waɗanda suka yi su za su zama kamar su, haka kuma zai zama da dukan waɗanda suke dogara gare su.
[19] Ya gidan Isra’ila, yabi Ubangiji; Ya gidan Haruna, yabi Ubangiji;
[20] Ya gidan Lawi, yabi Ubangiji; ku da kuke tsoronsa, yabi Ubangiji.
[21] Yabo ya tabbata ga Ubangiji daga Sihiyona, gare shi wanda yake zama a Urushalima. Yabi Ubangiji.