Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:10

[1] Me ya sa kake fariya game da mugunta, kai babban mutum? Me ya sa kake fariya dukan yini, kai da kake abin kunya a idanun Allah?

[2] Harshenka kan shirya hallaka; yana nan kamar reza mai ci, kana ta ruɗu.

[3] Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri, ƙarya a maimakon faɗin gaskiya. Sela

[4] Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa, Ya kai harshe mai ruɗu!

[5] Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka. Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka; zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. Sela

[6] Masu adalci za su ga su ji tsoro; za su yi masa dariya, suna cewa,

[7] “Yanzu, ga mutumin da bai mai da Allah mafakarsa ba amma ya dogara a yawan arzikinsa ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!”

[8] Amma ni kamar itace zaitun ne ina haɓaka a gidan Allah; na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah har abada abadin.

[9] Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi; a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau. Zan yabe ka a gaban tsarkakanka.

Zabura — Chapters