[1] Ka nuna wa ƙasarka alheri, ya Ubangiji; ka mai da nasarorin Yaƙub.
[2] Ka gafarta laifin mutanenka ka kuma shafe dukan zunubansu. Sela
[3] Ka kau da dukan fushinka ka kuma juye daga hasalar fushinka.
[4] Ka sāke mai da mu, ya Allah Mai Cetonmu, ka kau da rashin jin daɗinka daga gare mu.
[5] Za ka ci gaba da fushi da mu har abada ne? Za ka ja fushinka cikin dukan tsararraki?
[6] Ba za ka sāke raya mu ba, don mutanenka su yi farin ciki a cikinka?
[7] Ka nuna mana ƙaunarka marar ƙarewa, ya Ubangiji, ka kuma ba mu cetonka.
[8] Zan saurari abin da Allah Ubangiji zai faɗa; ya yi alkawarin salama ga mutanensa, tsarkakansa, amma kada su koma ga wauta.
[9] Tabbatacce cetonsa yana kusa da waɗanda suke tsoronsa, don ɗaukakarsa ta zauna a cikin ƙasarmu.
[10] Ƙauna da aminci za su sadu; adalci da salama za su yi wa juna sumba.
[11] Aminci zai ɓulɓulo daga ƙasa, adalci kuma yă duba daga sama.
[12] Ubangiji tabbatacce zai bayar da abin da yake da kyau, ƙasarmu kuwa za tă ba da amfaninta.
[13] Adalci na tafiya a gabansa yana shirya hanya domin ƙafafunsa.