Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:57

[1] Yabo ya tabbata ga Ubangiji dutsena, wanda ya horar da hannuwana don yaƙi, yatsotsina don faɗa.

[2] Shi ne Allah mai ƙaunata da kuma kagarata, katangata da mai cetona, garkuwata, wanda nake neman mafaka daga gare shi, wanda ya sa mutane a ƙarƙashina.

[3] Ya Ubangiji, wane ne mutum da ka kula da shi, ɗan mutum da har za ka yi tunaninsa?

[4] Mutum yana kama da numfashi; kwanakinsa suna wucewa kamar inuwa.

[5] Ka tsage sammanka, ya Ubangiji, ka sauko; ka taɓa duwatsu, domin su yi hayaƙi.

[6] Ka aiko da walƙiya ka watsar da abokan gāba; ka karɓa kibiyoyinka ka sa su gudu.

[7] Ka miƙa hannunka daga bisa; ka cece ni ka kuma kuɓutar da ni daga manyan ruwaye, daga hannuwan baƙi

[8] waɗanda bakunansu sun cika da ƙarya, waɗanda hannuwansu na dama masu ruɗu ne.

[9] Zan rera sabuwar waƙa gare ka, ya Allah; a kan molo mai tsirkiya goma zan yi maka kiɗi,

[10] ga Wannan wanda yake ba wa sarakuna nasara, wanda ya cece bawansa Dawuda. Daga takobin kisa.

[11] Ka cece ni ka kuma kuɓutar da ni daga hannuwan baƙi waɗanda bakunansu sun cika da ƙarya, waɗanda hannuwansu na dama masu ruɗu ne.

[12] Ta haka ’ya’yanmu maza a ƙuruciyarsu za su zama kamar tsire-tsiren da aka kula da su, ’ya’yanmu mata kuma za su zama kamar ginshiƙai da sassaƙa don adon fada.

[13] Rumbunanmu za su cika da kowane irin tanadi. Tumakinmu za su ƙaru ninki dubu, ninki dubu goma-goma a filayenmu;

[14] shanunmu za su ja kaya masu nauyi. Ba za a sami tashin hankali a katangarmu ba, ba zuwan zaman bauta, ba jin kukan damuwa a titunanmu.

[15] Masu albarka ne mutanen da wannan zai zama haka; masu albarka ne mutanen da Allah ne Ubangiji.

Zabura — Chapters